11 Agusta 2020 - 10:20
Lebanon: Wadanda Suka Samu Raunuka A Hatsarin Beirut Suna Isa Asibitin Wucin Gadi Na Iran

Mutanen birnin Beirut na kasar Lebanon wadanda suka ji rauni ko suka sami matsalar kiwon lafiya suna tururuwa zuwa asibitin tafi da gidanka na Hilal Al-ahmar na kasar Iran don karban magani da kuma jinya.

ABNA24 : Shafin yanar gizo na hukumar bada agajin gaggawa na kasar Iran, ya nakalto Husain Arifi shugaban tawagar hukumar zuwa kasar Lebanon yana cewa , mutane da dama wadanda suka hada da mutanen gari da kuma sojoji suna turuwa zuwa asibitin don karban jinya.

A ranar Asabar da ta gabata ce aka bude asbitin wucin gadi na kasar Iran a birnin na Beirut. Sannan kafin haka an kai magunguna da kayakin aiki na asibitin masu nauyin ton 95 da farko sannan aka kara wasu masu nauyin ton 60 har sau hudu.

Asibitin dai yana da sassa daban daban wadanda suka hada da bangaren kula na musamman wato ICU, bangaren tiyata, da kuma wani wuri dauke da gadajin masu jinya a asbitin.

A ranar tarlatan da ta gabata ce wata fashewa a tashar jiragen ruwa na Beirut ya haddasa mutuwar mutane akalla 156 sannan wasu kimani dubu 6 suka ji raunin.

Sannan har yanzun ana kokarin zakulo wadanda suka rage karkashin burbushin fashewar.

342/